Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce cututtuka marasa saurin yaduwa, da suka hada da cututtukan zuciya, hawan jini, ciwon daji, ciwon sukari da kuma cututtukan huhu, sune ke da alhakin kusan kashi 70% na duk mace-macen da ake samu a duniya.
Kusan kashi uku cikin hudu na mutuwar da ake samu sakamakon wadannan cututtuka, WHO ta ce kashi 82% na mutane miliyan 16 na mutuwa ne da karancin shekaru, ko kuma kafin su kai shekaru 70, abinda ya fi faruwa a kasashe matsakaita.
Yawaitar masu mutuwa sakamakon ire-iren wadannan cutuka ya samo asali daga abubuwa hudu masu hadari, wato shan taba, rashin motsa jiki, amfani da barasa mai cutarwa da abinci mara kyau.
Annobar dai a cewar WHO na haifar da mummunar illa ga harkokin kiwon lafiya da kuma kara barazana ga rayuwar al’umma.
WHO ta ce gwamnatoci na bukatar daukar matakan gaggawa don cimma burin kawar da barazanar cutuka marasa yaduwa ga rayuwar al’umma.
Ghana, Norway da WHO sun amince su yi aikin hadin gwiwa na gaggawa domin ceto rayuwakan al’umma daga cutuka marasa yaduwa da ke yin kisan mummuke.
RFI