Inyamuri ba zai gaji Buhari ba – Orji Kalu

0
120

Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Kalu a ranar Talata 20 ga watan Satumba ya ce babu wani Inyamuri da zai lashe zaben 2023 mai zuwa, wanda a bayyana ya yi fatan rasa nasarar Peter Obi.

Peter Obi, wanda dan takarar shugaban kasa ne a jam’iyyar Labour ya lashe zaben fidda gwanin jam’iyyar, kuma yana alfahari da yawan mabiya a Najeriya, musamman a kudancin kasar.

Duk da cewa bai da wata madafa da tsarin cin nasara, amma ya yi imanin cewa, jama’a masu goyon bayansa ne kashin bayan nasararsa.

Kalu ya zanta da manema labarai, ya ce batun shugabancin Najeriya ba na kabilanci bane, kuma a baya ya shawarci jam’iyyun siyasa su mika tikitin shugaban kasa Kudu maso Gabas.

A cewarsa; “Da suka ki yin hakan, kuma dake batun shugabanci ba na kabilanci bane, haka na hakura.

Ban da matsala dan Inyamuri ya zama shugaban kasa.

Amma ya kamata mu yi hakan da sauran ‘yan Najeriya.

“Idan bamu dama da sauran ‘yan Najeriya ba, hakan ba zai haifar da da mai ido ba kuma duk sanuwanka.

Shugaba ne na Najeriya ba shugaban yankin Inyamurai ba.”

Kalu ya kuma bayyana cewa, ai shi ma Inyamuri ne na gaske, kuma cikakken dan Najeriya, amma da za a zabi wani ya gaji Buhari a zaben 2023 to tabbas shine.

Legit