Wani Biri da ya tsinke ya addabi mutanen Janbulo dake Kano

0
106

Wani shu’umin Biri ya addabi mutanen yankin Janbulo 2nd Gate dake karamar hukumar Gwale a cikin Kano, sati guda kenan da tsinkewar birin daga wani gida harya addabi al’ummar dake unguwar ta Janbulo.

Birin dai ya Tsinke ne daga wani gida har yake shiga cikin gidajen jama’a ne yana yi musu barna ta kayyakin amfani hadda abinci da kuma tsoratar da matan aure.

‘’Wani mazaunin unguwar mai suna Abdullahi Ibrahim ya shaida wa Husalive cewa, ya ga mace da yayanta a waje tana neman taimako domin a fitar mata da birin daga gidan ta’’.

‘’ akwai wanda ya yi yunkurin kama wannan birin amma bai samu nasara ba, kuma birin har yaji masa mummunan rauni haka dole ya hakura yakyale shi.

Abdullahi Ibrahim ya kara da cewa birin ya fasa wa wata mata wayar ta hannu.

‘’ kazalika ya fasa gilashin motar wani mutum da duwatsu ‘’.

Yanzu haka dai hukumar gidan ajiyar namun daji ta Jahar Kano ta samu nasarar kama birin bayan an yi masa allura tare da tafiya da shi.

Mutanen yankin sun bayyana farin cikin akan wannan lamarin bayan kama shi da aka yi sakamakon barnar da yake yi mu su.

(Hausalive)