Atletico Madrid ta sha alwashin hukunta wadanda suka ci zarafin Vinicius Jr

0
139

Atletico Madrid ta yi tur da rera wakar da wasu ‘yan tsirarun magoya bayanta suka yi domin cin zarafin dan wasan Real Madrid Vinicius Junior, a wajen filin wasansu na Metropolitano, kafin karawar da suka yi a ranar Lahadin da ta gabata, inda Real Madrid din ta samu nasara da 2-1.

Atletico Madrid ta ce za ta ba da hadin kai a binciken da hukumomi za su yi, domin ganowa da kuma hukunta wadanda suka ci zarafin dan wasan.

A ranar Litinin, hukumar La Liga ta yi Allah wadai da ” kalaman nuna kiyayyar da aka furtawa matashin dan wasan, inda ta sha alwashin gurfanar da masu laifin.

Cin zarafin na ranar Lahadi ya biyo bayan kalaman da wasu masu fashin baki kan wasanni a Spain suka yi, inda suka soki salon yin rawa da dan wasan ke amfani da shi bayan jefa kwallo a ragar abokan hammaya.