Manyan yan takarar NNPP a Osun sun juya wa Kwankwaso baya, sun dauki Tinubu

0
163

Mutum hudu cikin wadanda za su yi takara a zaben 2023 karkashin jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, a Jihar Osun, a ranar Laraba sun bayyana goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na APC, Sanata Bola Tinubu.

Yan takarar, Clement Bamigbola, dan takarar sanata na Osun Central; Bolaji Akinyode, dan takarar sanata na Osun West; Olalekan Fabayo da Oluwaseyi Ajayi, yan takarar majalisar tarayya na Boluwaduro/Ifedayo/Ila, da Ijesa South kamar yadda aka jero.

Yan takarar hudu sun ce sun janye goyon bayansu ga Kwankwaso suka koma goyon bayan Tinubu saboda rufa-rufa da ake yi wurin gudanar da harkokin jam’iyyar a matakin kasa.

Da ya ke magana da yan jarida a Osogbo a madadin sauran yan takarar, Bamigbola ya ce:

“Duba da abubuwan da ke faruwa a jam’iyyar mu kuma bayan tuntubar da samun amincewar magoya bayan mu, muna son sanar da goyon bayan mu ga dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu.