Bayan kisan da a ke zargin wani ɗan China, Geng Quanrong ya yi wa wata budurwarsa ƴar jihar Kano, Ummukulthum Buhari, wata budurwa ta garzaya gurin ƴan sanda kan a yi mata tsakani da wani saurayinta ɗan ƙasar Turkiyya.
Budurwar, wacce a ka sakaya sunanta sabo da tsaro, ta garzaya shelkwatar ƴan sanda ta Jihar Kano, inda ta kai rahoton cewa ya matsa cewa sai ya aure ta, ita kuma ba ta so.
A cewar ta, kisan da a ke zargin Quanrong ya yi wa Ummukulthum, wacce a ka fi sani da Ummita ne ya tsorata ta, shi ne ta yanke shawarar ta shigar da ƙorafi ga ƴan sanda domin ai musu tsakani.
Ta shida wa rundunar ƴan sandan cewa saurayin nata na da zafin soyayya, inda har ya taba daɓa wa kansa wuƙa a kan ta, inda ta ƙara da cewa har ma ta yi iƙirarin cewa idan har bata aure shi ba to wani abu zai iya faruwa da ita.
“Shine nima na zo ma shigar da ƙorafi sabo da abinda aka yi wa Ummita ya tsorata ni. Ya addabe ni yana ta bibiya ta.
“Babu wani abu na kuɗi ko makamancin haka da ya taɓa shiga tsakanin mu amma ni ya matsamin.
“Watan mu uku kenan tare, ni so na ke a raba mu. Rannan ma har suka ya caka wa kansa kuma yace ni ma idan ban aure shi ba to wani abu zai iya faruwa da ni a rayuwa ta.
“Sabo da haka da Allah a raba mu da shi,” in ji ta.
A nasa ɓangaren, Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce Kwamishinan Ƴan Sanda na Jihar, Abubakar Lawan ya bada umarnin a yi binciken ƙwaƙwaf a kan lamarin.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su riƙa sanya ido da jajircewa a kan abubuwan da ke faruwa a tsakanin su.