PENGASSAN ta zargi sojoji da sa hannu a satar danyen mai da akeyi a Najeriya

0
95

Kungiyar manyan ma’aikatan bangaren man fetur da iskar gas a Najeriya ta zargi sojoji da kasancewa ummul’aba’isin yawaitar satar danyen mai a kasar.

Kungiyar ta yi wa Kwamitin da majalisar dattawar kasar ta kafa don gudanar da bincike a kan matsalar satar danyen mai a karkashin jagorancin Sanata Akpan Bassey ne wannan bayani

Shugaban kungiyar PENGASSAN na kasa, Festus Osifo ya ce jami’an sojin da aka bai wa aikin kare butatan man kasar ne suke hadin baki da bata gari wajen satar man, ta wajen bada kariya ga barayin da masu gudanar da kananan matatun mai.

Osifo ya yi zargin cewa ana yin wannan satar ce da sanin hukumomin da aka dora wa alhakin kula da da kadarorin main a kasar.

Ya ce bangaren sojojin da ke aikin tsaron ruwan kasar na Amphibious Brigade da kuma takwarorinsu na sojin ruwa da ke Fatakwal da kuma wasu manyaan jami’an soji suna da hannu dumu dumu a wannan danyen aiki na satar danyen mai.

Osifo ya ce bincike ya nuna cewa har ma jaami’an soji na baada cin hanci ga manyaansu don kawai a tura su aiki a wuraren da ake wannan badakalar a yankin Neja Delta.