SSS sun kuɓutar da mutane 27 da akai safararsu a Kano

0
103

Hukumar yan sandan farin kaya, SSS ta kuɓutar da mutane 27 da ake yunkurin safararsu ta kuma miƙa su ga hannun jami’an tsaro na haɗin-gwiwa da ke aiki a bakin boda, shiyyar Kano.

Abdullahi Babale, kwamandan shiyyar Kano na hukumar yaƙi da safarar mutane, NAPTIP ne ya faɗi haka a yayin wata gana wa da manema labarai a jiya Alhamis a Kano.

Ya bayyana waɗanda aka kuɓutar ɗin sun fito ne daga jihohin Oyo, Osun, Kogi, Ondo, Ekiti, Lagos da Ogun.

A cewar sa, waɗanda ake yunƙurin safarar ta su, da shi mai safarar ta su, na kan hanyarsu ne ta zuwa kasar Libya.

Babale ya ƙara da cewar, shekarunsu sun kai tsakanin 19 zuwa 40, inda ya ƙara da cewa 23 mata ne sai maza 4.

Ya kuma ce hukumar za ta gurfanar da wanda ake zargi da yunkurin safararsu, inda za ta sada waɗanda aka kuɓutar da iyalansu.