Tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar ya ja hankalin ‘yan kasar kan muhimmancin kare ‘yancinsu da kuri’arsu a babban zaben 2023.
Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, ya yi wannan kira ne a lokacin da yake shirin gudanar da taron sa hannu a yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin ‘yan takara na jam’iyyun siyasa gabannin yakin neman zabe.
Taron zai kuma kunshi sauran masu ruwa da tsaki inda za a sanya hannu a rukuni biyu.
Na gabanin fara yakin neman zabe da kuma gab da babban zaben kasar da za a gudanar a shekara mai zuwa.
A can baya dai an saba kulla irin wannan yarjejeniya tsakanin ‘yan takara kafin zabe.
Sai dai a wannan lokaci an ga sauyi, saboda tabbatar da cewa komai ya tafi a cikin lumana.
A can baya dai an saba kulla irin wannan yarjejeniya tsakanin ‘yan takara kafin zabe.
Sai dai a wannan lokaci an ga sauyi, saboda tabbatar da cewa komai ya tafi a cikin lumana.
Sannan ya ce wani aikin kwamitin nasu shi ne tabbatar da cewa ‘yan siyasa za su yi yakin neman zabe ba tare da tayar da hankali ko amfani da matasa ana ba su kwaya suna abubuwan rashin dacewa ba.
“Za mu tabbatar ba a yi amfani da ‘ya’yanmu da jikokinmu ba ana ba su kudi da kwaya suna aikata abubuwan da bai kamata ba.”
Janar din ya kuma nusar da ‘yan Najeriya cewa zaben 2023 wata muhimmayar dama ce ta yi wa kasa hidima da kareta domin wanzuwar ci-gaba mai dorewa.
A ranar Alhamis din mako mai zuwa ake sa ran cimma yarjejeniyar farko, sai kuma cikin watan Janairu za a cimma yarjejeniya ta biyu.
Abubuwan da ke kunshe a yarjejeniyar su ne yarda da sakamakon zabe da kuma kwantar da hankali wajen yin abubuwan da suka kamata, kama daga kamfen har zuwa lokacin zabe da bayan zaben.
BBCHAUSA