Ku dakatar da ni ayau idan kun isa – Wike ga PDP

0
107

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya faɗa wa jam’iyyar PDP cewa idan ta isa ta dakatar da shi daga jam’iyyar saboda abubuwan da yake yi na tayar da zaune tsaye a cikin jam’iyyar.

” idan sun isa su dakatar da ni a yau. Duk da cewar nasan ba za su iya ba, saboda sun san abin da zan iya yi. Kuma sun sani duk ɗan da ya hana mahaifiyarsa barci, to shi ma ba zai yi barci ba,” inji shi.

Wike ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da manema labarai kai tsaye a Fatakwal, inda ya ce jam’iyyar ta san abin da zai iya yi idan suka dauki wannan matakin korarsa ko dakatar da shi.

Gwamnan jihar Rivers ya zargi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu da girman kai wajen hakurkurtar da su da kuma cika masa sharuddan sa, wanda kin yin hakan ke kara dagula rikicin jam’iyyar gabanin zabe mai zuwa.

Ya kuma ce duk da kiraye-kirayen da magoya bayansa ke yi na cewa Ayu ya yi murabus ya kuma cika alkawarin da suka yi a baya na cewa tun da Atiku ya yi nasara zai yi murabus don share fagen samun daidaito da hada kai a jam’iyyar, Atiku da Ayu sun ki cika alkawarin da suka dauka.