Dan takaran zaben shugaban kasa a Najeriya na shekara mai zuwa a babbar Jam’iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar ya bayyana cewar Jam’iyar ta su zata samu nasara ba tare da gudumawar Gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike ba.
Atiku ya yi wadannan kalamai ne lokacin da ya ke ganawa da shugabannin kwamitin amintattun Jam’iyar wadanda ke kokarin sasanta barakar da aka samu tsakanin Atiku da Wike bayan zaben fidda gwanin da ya samu nasara.
Tun bayan zaben fidda gwanin da Atiku ya samu nasara, Wike da magoya bayan sa ke ci gaba da korafi akan zargin rashin adalci, yayinda suka gindaya wasu sharudda masu tsauri da su ke bukata a biya musu kafin goyawa Atiku baya a zaben shekara mai zuwa.
Daga cikin bukatun har da sauke shugaban Jam’iyyar PDP Iyorchia Ayu domin maye gurbin sa da wani dan kudancin Najeriya, tunda dan takaran shugaban kasa ya fito daga arewa, abinda wasu daga cikin ‘ya’yan Jam’iyyar ke cewa ba zai yiwu ba.
Atiku ya yi misali da zaben shekarar 2019 wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu nasara, inda ya ke cewa duk da ya ke shugaban bai lashe zaben Jihar Rivers ba, nasarar da ya samu a Jihohin Lagos da Kano da wasu jihohi sun taimaka masa zama shugaban kasa.
Yunkurin sasanta Wike da Atiku na ci gaba da zama babban kalubale ga shugabannin Jam‘iyyar PDP, yayinda ake rade radin cewar Gwamnan na Rivers na tunanin sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC mai mulki.
Daga cikin alamun kuwa, har da gayyatar da ya yiwa gwamnan Lagos Babajide Sanwo-Olu domin kaddamar da wasu ayyukan raya kasa da gwamnatin sa ta kammala, yayinda ya sake gayyatar tsohon Gwamnan Sokoto, Dr Aliyu Magatakarda Wamakko, wanda jigo ne a APC da ya je ya kaddamar da wasu ayyuka a makon gobe.
Masu sanya ido akan siyasar Najeriya na bayyana cewar ficewar Gwamna Wike daga PDP ba karamar illa za ta yiwa Jam’iyyar ba a zaben mai zuwa.