Shugabannin jami’o’i ba su da ikon bude makarantun da yajin aikin mu ya shafa – ASUU

0
79

Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta ce Shugabannin Jami’o’in Kasar mallakin Gwamnatin Tarayya ba su da ikon tursasa a bude jami’o’i a yanzu.

ASUU ta yi wannan furuci ta bakin babban jami’inta shiyyar Legas, Dokta Adelaja Odukoya, a ranar Litinin.

Wannan dai na zuwa ne bayan da Gwamnatin Najeriya ta umarci duk shugabannin jami’o’in kasar da ke karkashin kulawarta su koma bakin aiki tare da kyale dalibai su koma karbar darussa.

Da yake magana da wakilinmu ta wayar tarho, Dokta Odukoya ya ce shugabannin jami’o’in ko iyayen jami’o’in ba su da ikon bude jami’o’in kasar face Majalisun Gudunar da Harkokin Jami’o’in.

Gwamnatin Tarayyar dai ta ba da umarnin bude jami’o’i cikin wata takarda da Hukumar Kula da Jami’o’in Kasar NUC ta aika wa shugabannin jami’o’i mallakin Gwamnatin Tarayyar, wadda Babban Sakataren Hukumar ta NUC ya sanya wa hannu.

Sai dai Dokta Odukoya wanda Karamin Farfesa ne Sashin Kimiyyar Siyasa na Jami’ar Legas ya ce, babu jami’ar da ASUU ta rufe lokacin da ta tsunduma yajin aiki.

“ASUU ta shiga yajin aiki amma babu wata jami’a da ta taba rufewa.

“Amma kuma idan har ta kasance cewa Shugabannin Jami’o’in ne suka rufe jami’o’in ai ga mai fili ga mai doki nan suna iya budewa.

“Ba ni da labarin cewa an rufe jami’o’i, amma ina da tabbacin suna yajin aiki.

“Kaddara ma a ce an rufe jami’o’in ne, shin shugabannin jami’o’in ko iyayen jami’o’in za su iya budewa?

“Wannan ba aikin kowa ba face Majalisar Gudanarwar jami’o’in, kuma a hakikanin gaskiya wannan Majalisa ba za ta zauna ba matukar ana yajin aiki irin wannan na sai abin da hali ya yi.

“Saboda su kansu mambobin Majalisar ’ya’yan kungiyar ASUU ne kuma suna yajin aiki, saboda haka su kansu suna cikin wadanda Gwamnati ke kokarin tunzurawa.

“Wadanda suke da masaniya a kan tsare-tsaren jami’o’i sun san cewa shugabannin jami’o’i ba za su iya bude jami’o’in ba don ba a lokacin mulkin soja muke ba a yanzu.

“Wannan nauyi na bude jami’o’i ya rataya ne a kan Majalisar Gudanar da Harkokin kowacce jami’a, kuma muna wannan yajin aiki ne saboda a kawo tsari.

“Amma idan Buhari da ’yan kanzaginsa sun ga za su iya, suna iya zuwa su bude jami’o’in su koyar da kansu,” a cewar Dokta Odukoya.

Aminiya ta ruwaito cewam Gwamnatin Najeriya ta kai karar kungiyar malaman ta ASUU, inda a makon jiya kotun ta umarci malaman da su janye yakin aikin, sai dai kungiyar malaman ta daukaka kara, matakin da ka iya tsawaita wannan takaddama.

Tun a ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu ne ASUU ta tsunduma yajin aikin gargadi ga gwamnatin Najeriya na tsawon wata guda, sai dai daga baya kungiyar ta mayar da yajin aikin na Illa Masha Allahu.

An dai yi ta zaman sulhu tsakanin bangarorin biyu ba tare da an cimma wata masalaha ba.