Allah Ya karbi rayuwar Umar Malumfashi wanda aka fi sani da Yakubu Kafi Gwamna a cikin shirin Kwana Casa’in mai dogon zango.
Marigayin ya rasu ne a wani asibiti da ke unguwar Hausawa bayan Masallacin Murtala da ke Kano a Yammacin ranar Talata bayan sallar Magariba.
Tijjani Faraga, daya daga cikin manyan jaruman Kannywood da ya ziyarci mamacin a lokacin yana jinya ne ya tabbatar wa da jaridar Aminiya hakan.
Karin bayani na nan tafe