Gwamnati ta janye umarnin da ta bayar na sake bude Jami’o’i

0
92

Gwamnatin Tarayya ta janye umarnin da ta ba Shugabannin Jami’o’i da hukumomin gudanarwarsu na sake bude makarantun don dalibai su koma karatu.

Umarnin na farko dai na kunshe ne a cikin wata wasika da Daraktan Kudi na Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC), Sam Onazi, ya aike wa jami’o’in tarayya, a madadin Shugaban hukumar, Farfesa Adamu Rasheed.

A cikin wasikar dai mai dauke da kwanan watan 23 ga watan Satumban 2022, gwamnati ta umarci shugabannin jami’o’in su tabbatar malamai sun koma aiki gadan-gadan domin harkokin koyo da koyarwa su ci gaba a makarantun.

Sai dai daga bisani an janye umarnin a cikin wata sabuwar wasikar mai lamba, NUC/ES/138/Vol.64/136, wacce ita ma Sam Onazin ya rattaba wa hannu.

Sai dai da wakilinmu ya tuntubi Kakakin na NUC, Haruna Lawal Ajoh, ya ce an janye umarnin ne saboda wanda ya rattaba mata hannu mukaddashi ne a kan kujerar.

Kazalika, Haruna ya kuma ce Ministan Ilimi da Shugaban NUC sun tattauna sannan sun amince da janye umarnin.

“Bisa ga dukkan alamu har yanzu ana ci gaba da tattaunawa,” inji Kakakin na NUC.

Tun a watan Fabrairun bana ne dai Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta tsunduma yajin aiki kan zargin gwamnati da rashin cika mata wasu alkawuranta.

Kungiyar dai ta ce tana neman a inganta sakar wa jami’o’i kudaden gudanarwarsu ne sannan a biya su wasu hakkokin da suke bi da dai sauran bukatu.