Sama da kaso 70 na Katsinawa na fama da matsanancin talauci – MDD

0
80

Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da kaso 70 na al’ummar jihar Katsina na rayuwa cikin matsanancin talauci.

Shugaban sashin jinkai na majalisar a Najeriya, Mathias Schmale, ne ya bayyana hakan ga Gwamnan jihar, Aminu Masari, a ziyarar da ya kai masa ranar Litinin.

“A taron da za mu gudanar ranar Laraba, za mu tattauna al’amuran da suka shafi jinkai a Najeriya, ba iya Arewa maso Gabas kadai ba,” inji shi.

Schimale ya ce Gwamnan ya sha kai ziyara ofishin Majalisar domin nuna damuwarsa da halin da al’ ummar jihar ke ciki.

Ya kuma ce, “Ba mu manta kokarinsa ba, domin abin da na fahimci akwai matsalar karancin cin abinci mai gina jiki a Najeriya baki daya, ba iya jihar kadai ba.

“Sannan na gano ummul aba’isun matsalolin shi ne rashin tsaro da talauci. sai rashin ilimi a wasu wuraren.”

A nasa martanin, Gwamna Masari ya ce matsalar rashin abinci mai gina jiki a jihar na da alaka da wasu al’adu na al’ umma.

Ya ce, “A jihohin arewacin Najeriya da dama za ka ga iyali sun dogara ne da gonarsu da iya mutane 10 za ta iya ciyarwa, amma bayan shekaru 20 duk da sun hayayyafa, da ita dai za su ci gaba da ciyar da kawunansu.

“Haka suke dogaro da abincin da ba zai wadace su ba. Abin tambayar a nan shi ne ta yaya za mu kawo karshen matsalar?

“Sai muka yanke shawarar bada ilimin yadda mutane za su koyi dabarun nemna na kansu.