’Yan bindiga sun sace ’yan sanda 3 a Jihar Ogun

0
86

Rahotanni na cewa, ’yan bindiga sun sace wasu ’yan sanda uku da tsakar rana a yankin Wasinmi da ke Karamar Hukumar Ewekoro ta Jihar Ogun.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, ’yan sandan da lamarin ya shafa sun kai ziyarar aiki ce a babban ofishin ’yan sanda na Onikan Zone 2 da ke Jihar Ogun.

Bayanai sun ce, da misalin karfe 2:30 na rana ’yan bindigar suka yi awon gaba da ’yan sandan wadanda ake dakon zuwansu a babban ofishin ’yan sandan da ke Wasinmi.

Insfeta Oladipo Olayemi ne jagoran tawagar ’yan sandan daga Jihar Legas wadanda aka tura wani bincike a babban ofishin da ke Ogun.

Majiyarmu ta ce direban motar da ya dauko ’yan sandan ya tsallake rijiya da baya.

Tuni dai jami’an ’yan sandan jihar suka bazama a kokarin ceto abokan aikinsu da lamarin ya shafa.

Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi da ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce dan sanda daya yan bindigar suka sace.

“Dan sanda daya ne a cikin wadanda lamarin ya rutsa da su kuma yanzu haka mun bi sahun wadannan masu garkuwa.

“Don ba za mu zauna mu yi zugum ba, kuma muna da tabbacin za mu ceto duk wadanda lamarin ya shafa cikin aminci,” a cewarsa.