Atiku yayiwa Abuja tsinke, Tinubu, Kwankwaso da Peter basu kammala shiri ba

0
106

A yayinda yau Laraba ake fara kaddamar da yakin Neman zaben shugaban kasa a zaben 2023 ,Atiku Abubakar da gwamnonin PDP sunyiwa Abuja tsinke tun daren jiya zuwa wayewar garin yau.

Jaridar Hausa 24 ta gano cewa Atiku Abubakar da gwamnonin da suke cikin PDP sun yiwa Abuja tsinke ne domin kaddamar da kwamitin yakin Neman zabensa daga Nan Kuma a fara yakin Neman zabensa.

Jaridar Punch ta rawaito cewa taron Wanda zai gudana a babban cibiyar taro ta duniya Dake Abuja ,an Jiyo Tsohon shugaban majalisar dattijai ta kasa Bukola Sarki cikin daren jiya na gugar zana ga Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike Wanda ya fice daga cikin kwamitin yakin Neman zaben Atiku Yana cewa Tutsun da mutum Daya yakeyi a Jam’iyar PDPn ba zaisa su karaya ba .

Saidai wata majiya Kuma na cewa har zuwa yanzu babu wani shiri na fara yakin Neman zaben Bula Ahmad Tunubu na Jam’iyar APC da Rabiu Kwankwaso na jami’ar NNPP Mai kayan marmari da Peter Obi na labor party.

Amma a ganawarsa da manema labarai shugaban kwamatin yakin Neman zaben Tunubu ,Kuma Gwamnan jihar Plateau Simon Lalong yace tsare tsaren da suka fitar na fara nasu gangamin ba zai tabbata ba a lokacin da suka tsara farawa .

Haka itama Jam’iyar Labor Party ta shaida cewa har zuwa yanzu Bata kammala nata Shirin ba tukunna .yayinda ita Kuma Jam’iyar NNPP Bata ce komai ba.