Har yanzu Najeriya Bata Koma daidai ba a bangaren hasken lantarki tun bayan matsalar da takai kashe lantarkin da akayi a duk Najeriya ranar Litinin.
Zuwa daren jiya wata kiddiga da aka fitar daga Maikatar Makamashi ta kasa ya nuna cewa an samu damar farfado da karfin hasken Wutar lantarki Mega wat 38 daga cikin Mega wat dubu 3 da dari 7 da 13 da aka rasa gaba danyansa ranar Litini .
Wannan shine karo na 7 cikin shekarar Nan da aka samu irin wannan matsala a bangaren Makamashi a kasar Nan.
A ranar Lahadin data gabata an samu karfin hasken lantarki Mega 4,100 kafin daga bisani a ranar litinin ya dawo Mega dubu 3 da doriya a karshe Kuma ya sauka kasa gaba Daya a safiyar litinin.