Bani da masaniyar ko Tinubu yana Najeriya – Jigon kamfen na Tinubu, Oshiomole

0
120

Tsohon gwamna kuma minista Adams Oshiomole ya yi wata magana mai daukar hankali game dan takarar shugaban kasa na APC.

A cewarsa, bashi da masaniyar inda Bola Ahmad Tinubu yake a yanzu, don haka ba zai iya cewa komai game dashi ba.

An fara gangamin kamfen din 2023 a Najeriya, ‘yan siyasa sun fara tallata hajojinsu na gaje kujerar Buhari.