Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya bai wa ‘yan Najeriya tabbacin cewa ‘yan sanda za su yi aiki tare da takwarorinsu wajen tabbatar da babban zaben 2023 ya gudana cikin lumana.
Shugaban Sashen Ayyuka na Musamman na rundunar, DCP Basil Idegwu, ne ya bayyana haka a madadin Shugaban ‘yan sandan a wajen wani taron da ya shafi sha’anin tsaro wanda Gidauniyar Cleen tare da hadin gwiwar Gidauniyar Ford suka shirya a Abuja.
Alkali ya ce ‘yan sanda na ci gaba da aiki ba dare ba rana domin cim ma irin nasarar da aka samu yayin zabubbukan da aka gudanar a jihohin Osun da Ekiti da kuma Anambra, a babban zaben na 2023.
Ya ce, “Mun samu yabo daga jami’an sa-ido na gida da ketare game da yadda ayyukanmu suka gudana yayin zabukan Ekiti da Osun.
“Wannan wata alama ce da ke nuni da irin shirin da ‘yan sanda da takwarorinsu suka yi don tabbatar da sahihin zabe a 2023,” inji shi.
Ya kara da cewa ‘yan sanda na kokarin tuntubar masu ruwa-da-tsaki a sha’anin tsaro tare da musayar fahimta don yin aiki tare wajen samar da tsare-tsaren da suke taimaka musu kan ayyukansu.
Kodayake Alkali ya ce, lamarin tsaro abu me da ya shafi kowane dan kasa, ya ce hakan ma ya sa yake da muhimmanci a shirya tarukan tattaunawa a tsakanin al’umma.
Aminiya