CBN zai fara cire kudi daga asusun ’yan Najeriya da suka ci bashin gwamnati

0
101

Babban Bankin Najeriya ya ce zai fara cire kudi daga asusun bankin ‘yan Najeriyan da suka taba cin bashin gwamnati na noma.

Hakzalika, bankin zai cire kudi daga asusun gwamnatin wasu jihohi domin biyan bashin da aka ba su.

An ba ‘yan Najeriya da dama rancen kudi karkashin shirye-shirye da dama na noma a kasar nan.