Gwamna ya mayarwa Buhari martani kan siyawa jami’an tsaron jiharsa makamai

0
103

Gwamnan jihar Ondo Oluwarotimi Akeredolu yayi wa gwamnatin tarayya martani cewa nufinsa na siyan makamai ga rundunar Amotekun shine don bai wa jama’ar Ondo kariya.

Akeredolu ya bayyana cewa dalilan da hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya bayar na ci gaba da kin amincewa da amfani da nagartattun makamai da jamiā€™an tsaron jiharsa, ba su da ma’ana a yayin da ake fuskantar kalubalen tsaro a jiharsa.

The Nation ta rahoto, Gwamnan Ondo ya ce gwamnatin jihar Katsina ba ta musanta furucinsa na amfani da AK47 ba da ‘yan bangansu ke yi ba a lokacin horo.

Akeredolu ya tsaya kan cewa dole ne jamiā€™an tsaron Amotekun da ke da goyon bayan doka a kowane yanki na kasar nan su samu damar mallakar makamai kamar yadda masu laifi ke yi.