Kudin kasashe 5 da suka fi dalar Amurka da Euro daraja a duniya

0
116

Idan ana maganar kudin da ya fi ko wane kudi daraja a duniya sau da dama mutane kan dauka idan aka ce Dalar Amurka da Yuro magana ta kare, amma kuma ba haka lamarin yake ba idan aka yi da kudaden wasu kasashe a duniya da basu fi mutum ya daga ‘yan yatsunsa ya kirge su ba.

Akwai kudin kasashe biyar da su ka fi Dalar Amurka da Pound Sterling daraja.

Kuwaiti Dinar da Bahrain Dinar su ne kudin da su ka fi kowane daraja. A yau darajar Kuwaiti Dinar ta nunka na Dala fiye da sau uku a kasuwa, mutane da dama suna tunanin cewa Dalar Duk da cewa Dalar Amurka da irins Pound Sterling su na da daraja, abin da ake fada da turanci ‘Highest Currency’, kudin da suka sha gabansu, daga ciki akwai Dinarin Kuwait.

Dinaran kasashen Kuwait da Bahrai sun ninka Dalar Amurka sau 3.29 da 2.65. Haka zalika akwai kudin Omani Riyal wanda shi ma ya sha gaban Dalar ta Amurka.

Jordanian Dinar da Gibraltar Pound su ne suka cika rukunin sahun biyar na farko a wannan jeri.

A halin yanzu, Highest Currency ya nuna Pound Sterling, Euro, da Dalar Amurka su ne na shida, takwas da na tara a cikin kasashen da suka fi daraja a Duniya.

Wadanne kudi ne suka fi daraja a yanzu?

1. Kuwaiti Dinar 2. Bahrain Dinar 3. Omani Riyal 4. Jordanian Dinar 5. Gibraltar Pound 6. Pound Sterling 7. Cayman Island Dollar 8. Euro 9. US Dollar 10. Swiss Franc Swiss Franc, da Dalolin kasashen Brunei, Kanada, New Zealand, Australia da Fiji sun cira tuta.

Kudin Libyan Dinar shi ne kudin da ya fi kowane daraja a Afrika. 11. Brunei Dollar 12. Canadian Dollar 13. Australian Dollar. 14. Libyan Dinar 15. Singapore Dollar 16. New Zealand Dollar 17. Fijian Dollar 18. Brazilian Real 19, Israel New Shekel 20, Turkish Lira, Naira kuma na ci gaba da karyewa a kasuwa.

 

AMINIYA.