Manoma 14 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jihar Taraba

0
87

Manoma 14 sun rasu wasu da dama kuma sun bace a wani hatsarin kwalekwale a Karamar Hukumar Gassol ta Jihar Taraba.

Shi dai wannan hatsarin kwalekwale ya auku ne a lokacin da manoman ke kokarin girbe amfanin gona a gonakinsu da ambaliyar ruwa ta mamaye.

Wani ganau, Nadabo Karal,  ya ce an yi nasarar an gano gawarwaki 15 bayan hatsarin kwalekwalen da ke dauke da kimanin manoma 50.

Nadabo ya ce biyu daga cikin mamatan ’yan gida daya ne, kuma hatsarin kwalekwalen shi ne mafi muni da aka taba sama a yankin.

Aminiya ta samu bayani cewa an samu kifewar kwalekwale ne sakamakon ruwan sama da iska mai karfi.

Ibtila’in ya auku ne a kauyen Gwamtamu, bayan manoma a cikin kwalekwale 12 sun fito suna kokarin girbe abin da za su iya a gonakinsu na masara da suka yi ambaliya a ranar Alhamis.

Wasu daga cikin manoman sun fito ne daga kauyukan da ke makwabtaka da Kogin Binuwai wadanda ambaliyar ruwa ta shanye gonakinsu na masara.

Zuwa lokacin hada wannan rahoto, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya ce na su samu rahoto ba daga babban ofishinnsu da ke Gassol.