NAJERIYA @62: Na jinjinawa Yan Najeriya bisa hakuri da sukayi da gwamnatina – Buhari

0
98

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jinjinawa Yan Najeriya abisa hakuri da juriya da sukayi da gwamnatinsa tsawon lokacin da yayi Yana Mulkin kasa .

Buhari yayi wannan jawabin a lokacin da yake yiwa Yan kasa bayani akan nasarori da Kuma kalubalen da gwamnatinsa ta samu albarkacin ranar bikin zagayowar samun yancin kan Najeriya shekara 62 daga turawan Ingila .

Shugaba Buhari ya Kuma godewa Yan Najeriya abisa damar da suka bashi har ya samu damar darewa kan kujerar Mulkin Najeriya a shekarar 2015 .

Sannan cikin jawaban nasa ,yace wannan shine karo na karshe a mulkinsa da yake yiwa Yan kasa bayani akan ranar Samun yancin Kai

Daga Nan yace ya samu gagarumar nasara a yaki da matsalolin tsaro da Kuma cin hanci da rashawa ,duk da tarnakin da annobar Corona Virus tayiwa gwamnatinsa da sauaran kasashen Duniya.

Wakilin Jaridar Hausa 24 da ya bibiyi jawaban na shugaban Kasa ,ya rawaito cewa , shugaba Buhari ya Kuma tabbatar dacewa gwamnatinsa zatayi duk Mai yiyuwa domin ganin anyi zaben 2023 cikin nasara da tsafta .

A bangaren tattakin arziki , shugaban yace gwamnatinsa ta baiwa masu zuba jari daga kasashen waje cikakkiyar dama domin bunkasa tattalin arziki Wanda Shima yace annobar ta Coronavirus ta kawo tarnaki.

Ya nemi Yan Najeriya da kada su karaya sannan Kuma hakurin da sukayi da matsin da aka samu Kai a ciki ba zai Fadi kasa banza ba .