Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU dake yajin aiki da suyi hakuri su Koma aiki.
Shugaban ya Kuma basu tabbacin shawo kan matsalolin da suke fama da su duk da irin matsalolin karancin kudaden gudanarwa.
Shugaban wanda ya sake nanata wannan kiran a wani jawabi da ya yiwa al’ummar Najeriya a ranar Asabar domin bikin ranar murnar samun yancin Kai Shekaru 62 a Abuja, ya ce ya ji takaicin yadda ake ci gaba da samun tabarbarewar harkokin ilimin manyan makarantun kasar nan.
Wannan jawabi da shirye-shiryen, wani bangare ne na ayyukan bikin murnar cika shekaru 62 da Najeriya ta samu ‘yancin kan ta daga kasar Ingila.
A cewarsa, Gwamnatin tarayya za ta ci gaba da hada-hadar albarkatun kasa da kasa wajen samar da tallafin ilimi domin tabbatar da cewa ‘yan kasa sun samu ilimi da kwarewa a sana’o’i daban-daban.
“Ya zama wajibi tabbas ina mai takaici game da irin ttashin-tashinar da ake ta fama da ita a tsarin karatunmu na manyan makarantu.
“Ina amfani da wannan rana na ranar samun ‘yancin kai wajen sake nanata kira na ga Kungiyar Manyan Malaman Jami’o’i da ke yajin aiki da su dawo ajujuwa tare da ba su tabbacin shawo kan matsalolin da suke fama da su cikin karancin albarkatun da ake fama da su.
A bangaren kiwon lafiya “Kamar yadda kuka sani, Najeriya na daya daga cikin kasashen da suka yi fatali da hasashen duniya game da tasirin tattalin arzikin da annobar cutar COVID-19 saboda juriya da jajircewa da muka yi akan cutar.”
Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin sa ta fara tunkarar matsalolin da suka shafi muhalli a fadin kasar domin dakile tasirin sauyin yanayi ta fuskar ambaliyar ruwa, zaizayar kasa, kwararowar hamada, gurbacewar iska da dai sauransu.
A bangaren sufuri kuwa Shugaba Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ci gaba da inganta hanyoyin sifirin jiragen kasa domin kara bude kofa ga al’umma kan harkokin tattalin arziki.
Ya ce tuni aka kammala ayyuka da dama na muhimman ayyukan layin dogo kuma a lokaci guda, an gyara tare da inganta kayan aikin da suka bukaci sauyawa kasancewar sun tsufa sosai.