Ina fatan ganin ƴan takara mata da matasa a zaɓen 2023 – Buhari

0
121

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya na son ganin an samu ƙaruwar mata da matasa a zaɓen 2023.

Ya bayyana haka ne a jawabinsa na ranar ƴancin kai ga al’ummar kasa a jiya Asabar.

Buhari ya kuma shawarci matasa da su guji tada zaune tsaye yayin da shekarar zaɓe ke ƙarato wa.

“Ina kuma so in bayyana fatana na ganin mun ƙara samun shigar mata da matasa a zaɓukan da ke tafe. Ina da tabbacin cewa matasanmu masu kuzari da hazaka, a yanzu sun gane cewa tashe-tashen hankula gaba ɗaya sun lalata harkar zaɓe, don haka ya kamata su daina bari ƴan siyasa na amfani da su don yin hakan,” inji shi.

Ya kuma yi kira ga ƴan siyasa da su guji kalaman da ba su dace ba a yayin gangamin yakin neman zabe, inda ya shawarce su da su rungumi yin kamfen da ayyukan da su ka yi na ci gaban al’umma gabanin zaben badi.

Buhari ya kuma bukaci ƴan Najeriya da su nemi ayyukan da ya shafi ƴan kasa daga hukumomin da ke riƙe da madafun iko.