Sharri ne, ban ci kudin wanda ya kai ni kara kotu ba – Hadiza Gabon

0
120

Fitacciyar Jarumar masana’antar Kannywood Hadiza Aliyu wadda aka fi sanida Hadiza Gabon ta ƙaryata batun cewa ta damfari wani da sunan za ta aure shi.

Jarumar ta bayyana haka ne cikin wani shiri amsoshin takardu da ake gabatarwa.

A yayin shirin wani cikin masu sauraron ta, ya tambaye ta shin ko ta biya kudin da akace ta damfari wani da zimmar za suyi aure?

Jarumar ta bayyana cewa ni babu abinda na biya domin banci ba, ta yiwu ma wanda yace naci masa shi zai bani wani abu domin batamin suna

Gabon ta bayyana cewar da kudin take so tana da hanyar da zata sami kudi fiyeda wanda ya kaita kara yace ta cimasa kuma ta hanyar halal a cewar ta.

 

Alfijir.