EFCC ta kwato motoci 15 da na’u’rori daga hannun masu damfarar yanar gizo-gizo a Jihar Delta

0
90

Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annuti (EFCC) sun kama wasu mutane 95 da ake zargi da damfarar yanar gizo a garin Warri na jihar Delta.

An kwato wayoyi iri daban-daban, kwamfutoci da kuma motoci 15 iri daban-daban da kudinsu ya kai Naira miliyan 300 daga hannun wadanda ake zargin, kamar yadda hukumar EFCC ta bayyana.

An kama wadanda ake zargin ne a wani samame da jami’an shiyyar Fatakwal na hukumar EFCC suka kai, in ji kakakin hukumar, Wilson Uwujeren.

Ya ce an kama wadanda ake zargin ne a yankin Adesa Ughonton da Jedda na Warri, jihar Delta bisa zargin zamba a intanet.

Ya ce, za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike kan motocin da sauran kayayyakin da aka kwato daga hannunsu.