Buhari ya zargi ASUU da hannu a almundahanar jami’o’i

0
80

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya zagi Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) da hannu cin hanci da aringizo da ake yi a jami’o’i.

Buhari ya zargin cewa “Sannan wadannan masu  yawan tafiya dogon yajin aiki su ma suna da laifi a wannan matsalar.”

Ya ci gaba da cewa, “Abin mamaki shi ne masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi, ciki har da kungiyoyi,  ba su mayar da hankali kan irin almundahanar da ake yi a bangaren kudaden shiga da jami’o’i ke tararawa ba.

“Ina kiran su da su tambayi hukumomin gudanarwar jami’o’in, sannan sun bincika irin aringizon da ake yi na ma’aikata da kudaden da ake kashewa, a makarantun.”

Ya bayyana cewa almundahana da ke yi a bangaren ilimi na yin zagon kasa ga kudaden da gwamnati ke sanya wa a bangaren.

A cewarsa, maimakon karkatar da hankali kan kason da ake ware wa jami’o’i a kasafin shekara-shekara, ya kamata masu sanya ido kan bangaren su fadada bincikensu zuwa kudaden da ake kashe wa bangaren.

Ya bayyana haka ne a jawabinsa na bude Taron Kasa kan Rage Almundahana, wanda Hukumar Yaki da Zamba da Dangoginsu (ICPC) at shirya da hadin gwiwar Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya da Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB).

Zargin nasa na zuwa ne bayan kungiyar ta shafe wata bakwai tana yajin aiki tun ranar 14 ga watan Fabrairu kan rashin biyan bukatunta.

Shugaban kasar ya sha yin kira ga kungiyar da ta janye yajin aikinta, amma ta ce allambaram.

Ya bayyana cewa: “Taron bana zai yi kallon kwakwaf kan yadda almundahana da aringizo ke zagon kasa ga tsare-tsaren ilimi da kudaden da ake sanyawa a bangaren wadanda ke jefa karatun matasan kasar nan cikin tasku.

“Yawan yajin aikin da manyan makaranu ke yi na nuwa wa jama’a kamar gwamnati ba ta wadata bangaren ilimi da kudade.

“Amma ya zama wajibi in fada cewa irin almundahanar da ke bangaren ilimi, tun daga matakin firamare har zuwa manyan makarantu su ke kawo cikas ga kudaden da ake sanyawa a bangaren.”

“Amma tsarin mulki na 1999 ya fifita bangaren ilimi wanda ya sanya a cikin jerin ayyukan yau da kullum.

“Hakan ya dora wa kasafin kudi da kuma gwamnait alhakin bayar da muhimmanci ga bangaren ilimi mai nagarta a matakin jiha da Gwamnatin Tarayya.

“Abin da ake ware wa a kasafin shekara na da nasaba da karfin aljihun gwamnati da sauran nauyin da ke kanta, wanda hakan ke yin tasiri ga kason da bangaren ilimi ke samu.

“Ya kamata a daina takaita lissafin kason bangaren ilimi zuwa abin da aka ware wa Ma’aikatar Ilimi da jami’o’i kadai.

“Ya kamata a rika hadawa da kason da ake ware wa bangern ilimi a matakin farko da na Asusun Raya Jami’o’i (TETFUND) da kudaden da ake mayarwa zuwa asusun TETFUND daga harajin ilimi,” in ji shi.

 

AMINIYA