Gwamnatin Lagos ta sanar da karin allbashi ga ma’aikatan jihar

0
79

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, a ranar Talata ya sanar da shirin karin albashi ga ma’aikatan jihar.

Mai taimaka wa Sanwo-Olu kan harkokin yada labarai, Jibril Gawat, wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter, ya ce gwamnan ya bayyana hakan lokacin da ya gana da ma’aikatan gwamnatin jihar.

Gawat ya rubuta cewa: “Gwamnan jihar Legas, Mista @jidesanwoolu a yau ya gana da ma’aikatan gwamnatin jihar Legas.

Gwamnan ya kuma sanar da karin albashin ma’aikatan.”