Kamfanin NNPC ya samu ribar biliyan N674 a wata 12

0
79

Kamfanin mai Kasa (NNPCL) ya sanar da samun ribar Naira biliyan 674 a shekarar kasuwanci ta 2021.

Babban Shugaban NNPLC, Mele Kolo Kyari, ya ce biliyan N674 da kamfanin ya samu bayan biyan haraji ya zarce ribarsa ta biliyan N287 ta shekarar 2020 da kashi 134.8 cikin 100.

“Ina farin cikin sanarwa cewa ribar  NNPC ya karu a shekara guda daga Naira biliyan 287 a 2020 zuwa Naira biliyan 674 bayan biyan haraji a 2021, wanda shi ne kashi 134.8% a shekara guda.

“Mun samu gagarumar bunkasa ta bangaren ribar kasuwanci a shekara uku da suka gabata,” a cewar Kyari.

Ya ce ayyukan bangaren hakar danyen mai ya yi tasiri matuka wajen samun wannan nasara.

A cewarsa, ba don matsalar masu satar danyen mai da ke janyo wa kamfanin asarar gangar danyen mai 200,000 a kullum ba, da ribar 2021 ta zarce haka.

Ya bayyana cewa NNPCL na da karfin samar da gangar danyen mai miliyan 2.4 a kullum, amma ayyukan masu fasa bututu sun sa  an rage adadin zuwa ganga miliyan 1.2.