ASUU da Gwamnati: Kotun daukaka kara za ta zauna kan hukuncin kotun ma’aikata

0
89

Kotun daukaka kara ta Tarayya ta sanya ranar Alhamis domin sauraron bukatar kungiyar malaman Jami’a ta Kasa (ASUU) na soke umarnin da kotun ma’aikata ta yi ba ta na janye yajin aiki.

A watan Satumba ne dai kotun ma’aikatan ta umarci ASUU ta janye yajin aikin da take gudanarwa, hukuncin da bai yi wa kungiyar dadi ba, inda suka garzaya kotun daukaka kara.

A zaman kotun na ranar Laraba, Mai Shari’a Hamma Barka da ke jagorantar wasu alkalan biyu, ya sanya ranar Alhamis domin sauraron shari’ar.

Hakazalika daya daga cikin alkalan, Biobele Georgewill ya shawarci lauyoyin bangarorin biyu da su tattauna, domin lalubo hanyar sasantawa a wajen kotun.

“A matsayinku na manyan lauyoyi, ya kamata ku duba yaran nan, da ma sauran lauyoyinmu, ku tattauna a junanku, ku kyale masu shari’a, ko samu amintacciyar hanya daya.

“Idan kuka yi haka, kasar ma baki daya za ta fi alfahari da ku”, in ji Goergewill.

A nasa bangaren lauyan gwamnatin, James Igwe (SAN) Igwe ya ce yana da yakinin shi da lauyan ASUU, Femi Falana (SAN), za su cimma matsaya kafin zaman kotun na ranar Alhamis.

Shi ma dai Falanan ya ce yana fatan a samu hanyar warware lamarin cikin lumana.