Kwamitin amintattu na PDP ya gaza cimma matsaya da Wike

0
71

An gaza cim ma matsaya yayin taron sulhu da aka gudanar tsakanin Kwamitin Amintattun na Jam’iyyar PDP da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike.

Mukaddashin Shugaban Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar PDP, Sanata Adolphus Wabara ne ya yi wannan karin haske dangane da tattaunawa a ranar Talata.

Wabara ya bayyana haka ne sa’ilin da yake yi wa manema labarai karin haske dangane da ganawar sirrin da suka yi da Gwamna Wike a ranar Talata.

Taron wanda aka gudanar a Fadar Gwamnatin da ke Fatakwal, babban birnin jihar, an yi shi ne ba tare da bai wa manema labarai zarafin shiga zauren taron ba.

Mambobin Kwamitin Amintattu na PDP sun nemi ganawa da Gwamna Wike ne a matsayin wani mataki na dinke barakar cikin gidan da PDP ke fama da ita.

Yayin taron, daga bisani an fahimci Gwamna Wiki ya bukaci a bai wa ‘yan jarida damar shiga taron bayan da ya nemi hakan a wajen abokan zaman nasa amma Wabara ya ki amincewa.

Bayan shafe kimanin sa’o’i hudu ana gudanar da taron, a karshe an ga mahalarta sun fito da alamar murmushi a fuskokinsu.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai Wabar ya ce, “Mun yi tattaunawa mai ma’ana.

“Ba mu cim ma matsaya ko ba. Kun san abu ne mai sauki a tattauna, amma yakan dauki lokaci kafin a samu masalaha.”