Muna gab da ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen Tinubu – Abdullahi Adamu

0
119

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta ce nan gaba kaɗan za ta sanar da ranar da za ta kaddamar da yakin neman zaɓen dan takararta na shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

A ranar Laraba ne jiga-jigan jam’iyyar suka yi wani zama a Abuja, inda suka daidaita a kan gangamin yakin neman zaɓen, wanda a baya wasu gwamnonin da kuma shugabannin jam’iyyar suka nuna ba su gamsu da tsarin da aka yi ba, sakamakon zargin cewa an mayar da su saniyar ware.

Sai dai Sanata Abdullahi Adamu, wanda shi ne shugaban Jam’iyyar APC a Najeriya ya bayyana wa BBC cewa tuni suka shawo kan matsalar da ta kunno musu kai.

Sanata Adamu ya bayyana cewa tun da farko matsalar ta samo asali ne daga sunayen da aka fitar na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa inda wasu suka rinƙa ƙorafi a kan sunayen.

Ya bayyana cewa ƙorafin ya fito ne daga bakin wasu daga cikin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da gwamnoni wanda hakan ya sa aka zauna domin tattaunawa a kan lamarin.

“Duka mun haɗu mun yi maganganu masu ma’ana, an gaya wa juna gaskiya daidai gwargwadon iyawarmu kuma an samu fahimta,” in ji Sanata Adamu.

Haka kuma ya bayyana cewa don sauran jam’iyyu sun ƙaddamar da yaƙin neman zaɓensu ba lallai bane APC a ce ita ma dole ta ƙaddamar da nata ba sakamakon kowace jam’iyya takunta daban.

Sanata Adamu ya kawar da zargin da ake yi kan cewa Tinubu na ƙasar waje ba shi da lafiya inda ya ce shi bai taɓa jin zancen cewa bai da lafiya ba, amma don tafiya ƙasar waje ya tabbatar da hakan.

Tun a ranar 28 ga watan Satumba ne hukumar zaɓe ta Najeriya wato INEC ta ɗage haramcin da ta saka na yaƙin neman zaɓe inda tuni wasu jam’iyyun suka soma yaƙin neman zaɓen.

A watan Fabrairun 2023 ne ake sa ran gudanar da zaɓen shugaban Najeriyar inda jam’iyyu da dama za su fafata.

Cikin waɗanda ke kan gaba a takarar akwai Bola Ahmed Tinubu na Jam’iyyar APC da Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP da Rabiu Musa Kwankwaso na Jam’iyyar NNPP da kuma Peter Obi na Jam’iyyar LP.