Buhari ya gabatar da kasafin kudi na 2023

0
72

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya gabatar da kasafin kuɗi na 2023 da ya kai naira tiriliyan 19.76 a gaban gamayyar majalisun dokokin kasar ranar Juma’a.

Kasafin shi ne na ƙarshe da shugaban ya gabatar yayin da yake shirin kammala wa’adin mulkinsa na biyu a ranar 29 ga watan Mayun 2023, yana mai cewa “ina son na bar abin tarihi a kasar fiye da yadda na same ta a 2015”.

Wannan ne kasafin kuɗi mafi yawa a tarihin Najeriya, inda ya zarta na shekarar 2022 da kashi 15.37 – wanda aka gabatar kan naira tiriliyan 17.13.

Kasafin kuɗin yana da giɓin da sai gwamnati ta hada da rance za ta cike fiye da rabin sa, wanda ya kai tiriliyan 12.

Ministar Kuɗi Zainab Shamsuna ta ce gwamnati za ta cike gɓin ne ta hanyar ciyo bashi da kuma sayar da wasu kadarorin gwamnati.

Kazalika akwai batun tallafin man fetur, wanda shi ma ƙarin dawainiya ne ga kasafin, wanda zai iya janyo zazzafar muhawara, kasancewar wasu na goyon bayan gwamnati ta ci gaba da ba da shi, yayin da wasu ke ganin ya kamata a dakatar, saboda a nasu ra’ayin masu hada-hadar man sun fi talaka cin gajiyar tallafin.

Sai dai ƴan majalisar da dama na da ra’ayin cewa akwai bukatar a jira a ga gangariyar abin da kasafin ya kunsa.

Honarabul  Jafar Sulaiman Ribadu, ɗan majalisar wakilai ne daga Jihar Adamawa wanda ke cewa zai so su karbi kudirin kasafin kudin da zuciya daya.

Amma Sanata Adamu Muhammad Bulkachuwa ya tabbatar da cewa an samu cikas wurin aiwatar da kasafin kuɗin bana a wasu ɓangarorin saboda rashin samun isassun kuɗin da za a aiwatar da shi.

Sai dai ya ce ana sa ran kafin ƙarshen shekara za a samu shigowar wasu kuɗin da za a ci gaba da ayyuka.

Za a iya cewa zumuɗi da ɗokin sauraron kasafin kuɗin na shekara-shekara ya ragu a tsakanin ‘yan Najeriya da dama, sakamakon yanke ƙaunar da wasu ke yi suna zargin cewa da yawa faɗa ne kawai ba cikawa.