Gwamnatin Kogi ta yi ikirarin mallakar kamfanin siminti na Obajana kuma ta fara yunkurin ƙwato shi daga hannun Dangote

0
109

Gwamnatin Kogi ta fara ɗaukar gaɓaran ƙwato kamfanin siminti na Obajana daga hannun kamfanin siminti na Dangote.

Kudurin gwamnatin na kunshe ne a cikin rahoton kwamitin kwararru na musamman don tabbatar da halascin mallakar kamfanin siminti na Obajana zuwa na Dangote.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya rawaito cewa an mika cikakken rahoton ga gwamna Yahaya Bello na Kogi a watan Satumba.

Sakatariyar gwamnatin jihar (SSG), Folashade Ayoade ce ta gabatar da rahoton a yau Alhamis a Lokoja.

Ayoade ta ce, ” ƙwato kamfanin siminti na Obajana Plc daga kamfanin Dangote Cement Company Limited ya zama wajibi a wannan lokaci.”

SSG ɗin ta gabatar da takardu cewa maida Obajana zuwa ga kamfanin Dangote “Ba halastacce ba, kuma rusasshe ne”.

Ta bayyana cewa a cikin rahoton, an nuna yadda a ka yi amfani da amfani da takaddun mallaka guda 3 na Kamfanin Simintin Obajana, mallakin gwamnatin Jihar Kogi, inda Dangote ya yi amfani da hakan ya ciyo bashin Nairq biliyan 63bn.

A cewarta, kwamitin bisa ga binciken da ya gudanar, ya bayar da shawarar cewa jihar Kogi ta dauki matakin kwato kamfanin siminti na Obajana daga hannun Dangote.