Kasafin Ƙudi: Buhari da Osinbanjo zasu kashe naira biliyan 3.34 a tafiye-tafiye da za suyi a 2023

0
102

Naira biliyan 3.34 fadar shugaban ƙasa ta ware dan tafiye-tafiyen gida da na waje na shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a cikin daftarin kasafin kudin shekarar 2023, da aka mika wa zaman hadin gwiwa na majalisar tarayya a ranar Juma’a nan.

Yadda daftarin kasafin kuɗin zai kasance shine: N2.49bn da aka ware don tafiye-tafiyen shugaban kasa, N862,076,448 ita kuma a tafiye-tafiyen cikin gida, yayin da tafiye-tafiyen kasa da kasa kuma zata lamushe N1,633,464,208.

Jumular N846,607,097 ita kuma zata tafi a rangadin Osinbajo, in da N330,320,396 zata tafi a tafiye-tafiye cikin gida, sai kuma N516, 286,701 a tafiye-tafiye kasashen waje. Kudin kasafin kudin 2023 ya kuma nuna cewa shugaban kasa da mataimakinsa za su kashe Naira 179,277,423 don abinci da abin sha. Za’a kashe Naira 301,138,860 wajen sayen kayan abinci a karkashin buƙatun yau da kullum da kuma wani N30,652,500 da aka ware domin sauran buƙatu.

Hakazalika Osinbajo zai kashe N156,662,400 don siyam kayan abinci. Da kuma wasu ƙarin N20,264,397 kan N2,350,626 da aka ware dan siyan kayan Sha, Man gas da dai sauran buƙatu.

Sauran kuɗaɗen da ake sa ran kashewa a ofishin mataimakin shugaban kasa, sun hada da naira miliyan 30,262,066 na tukuici ga ma’aikata da kuma alawus-alawus ɗinsu; sai kuma N18,888,552 akan tallace-tallace; da ƙarin N1,680,377 kan bukatun sadarwa; sai N23,211,005 dan walwala da jin dadin ma’aikata; da kuma N5,488,832 kan ayyuka da wasanni. Akwai Wasu kuɗaɗen da aka warewa Fadar gwamnati, wanda adadin su yakai N7,200,045,297 dan kula da na’urorin da lantarki na tsawon shekara, da kuma Naira 393,661,239 da aka ware domin ci gaba da gina sashen kula da lafiyar shugaban kasa.

A cikin daftarin, fadar shugaban kasa da dukkanin hukumomin da ke karkashin fadar gwamnatin jihar za su kashe naira biliyan 133,730,697,750 musamman kan ma’aikata, da wasu manyan bukatu.

Daftarin ya nuna nuna cewa Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin ƙasa Ta’annati (EFCC) ce ke da kaso mafi tsoka, wanda ya tasarma N43,201,071,521 da aka ware domin ma’aikatanta ku ma wasu buƙatunta. A inda kuma sauya motocin gwamnati da wasu abubuwa masu kama da haka zasu lashe N1,904,388,461.

 

Legit