Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na Ƙasa ya rasu a Canada

0
67

Vanguard ta ruwaito cewa Ogbulafor ya rasu ne a ranar Alhamis a kasar Canada yana da shekaru 73.

Idan za a iya tunawa, Marigayin shine Sakataren Jam’iyyar PDP na farko. Shi ɗan asalin garin Olokoro ne daga karamar hukumar Umuahia ta Kudu a Jihar Abia.

Ogbulafor, wanda aka haifa a ranar 24 ga watan Mayun 1949, shine sakataren PDP na kasa na farko, kafin daga baya ya zama shugaban jam’iyyar na kasa.

Amma, an tilasta wa marigayin yin murabus daga mukaminsa bayan rashin jituwa ya shiga tsakaninsa da wasu jiga-jigan PDP.