Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta na kashe tsabar kudi har dalar Amurka miliyan 10 a karkashin shirinta na ciyar da yara ‘yan makarantun firamare miliyan 10 da ke sassan kasar a wani yunkuri na karfafa gwiwar yaran don mayar da hankali a karatu.
Ministan kwadago da samar da ayyukanyi na Najeriyar, Chris Ngige wanda ke sanar da wannan alkaluman yayin karbar bakoncin jakadar Amurka a kasar Mary Leornard a ofishin sa da ke Abuja, ya ce matakin na da nufin magance matsalolin yaran.
Mininistan ya ce gwamnatin Najeriya ta samar da shirin ciyar da yara a makarantu ne don magance bautar da su a zamanance da ake yi da sunan aikatau ta hanyar mayar da su makarantu.
Ngige ya ye gwamnati ta samar da shirye-shiryen ne domin yaki da talauci, da kuma kwadaitar da yara karatu baya ga kawar da matsalar bautarwa ga yaran musamman a karkara.
Ministan ya ce a yanzu akwai yara ‘yan makaranta kimanin miliyan goma da ke cin gajiyar wannan shirin a sassan Najeriya musamman a yankunan karkara.