Zaben 2023: Ansamu musayar yawu tsakanin Mansurah Isah da Rahama Sadau akan siyasa

0
126

A daidai lokacin da aka fara kamfe, kamar yadda aka saba ana samun sabani tsakanin bangarori.

Aminiya ta gano akwai sabani a tsakanin taurarin Kannywood, inda akan samu sabani tsakanin magoya bayan jam’iyyu, kuma akan samu bambanci ra’ayi a cikin jam’iyya daya.

An samu cacar bakin ne saboda sunayen matan da za su yi kamfen din dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar APC.

A cikin jerin sunayen da aka fitar na masu nishadi da tallata Bola Ahmad Tinubu, akwai kusan ’yan fim da mawaka 33 da aka zakulo daga Masana’antar Kannywood da Nollywood a matsayin masu nishadi bangaren mata.

A cikin jerin sunayen matan Kannywood, akwai sunan Rahama Sadau, wanda hakan ya jawo ce-ce-ku-ce.

Ganin sunanta a cikin jerin ya sa Rahama Sadau ta fito ta nesanta kanta da tallata dan takarar.

A cewarta, “Wannan ba karamar karya ba ce. Ni ba ni da masaniya kan wannan. Ban ma san yaya aka yi sunana ya shiga cikin jerin sunayen nan ba, kuma ko kadan ba ni da alaka da shi,” kamar yadda ta bayyana a shafinta na Tuwita.

Sai dai hakan ya jawo martani da dama, inda Ali Nuhu ya rubuta cewa, “Haba Hajiya Rahama Sadau!”

Shi ma Furodusa Uzee Usman ya ce, “Sai ka ce dole.

Sannan ita ma Hadiza Gabon ta ce, “Kamar dole. Ikon Allah.”

Sai dai Mansurah Isah wadda ita ma take cikin jerin sunayen ta mayar da martani, inda ta ce duk da cewa an yi kuskuren sanya hotonta, asali ba sunanta ba ne a ciki.

A cewar Mansurah, “Zuwa ga Rahama, sunan da kika gani a jerin sunayen, asali ba sunanki ba ne.

Rahama MK ce aka saka, amma kasancewar sun fi saninki a matsayin Rahama a Kannywood, sai suka dauka ke ce. Amma kada ki damu, ba ke ba ce.”

Domin tabbatar da hakan, Mansurah ta wallafa wani jerin sunayen, wanda ta ce shi ne asalin jerin sunayen da aka fitar, inda a ciki Aminiya ta lura akwai sunan Rahama MK, babu sunan Rahama Sadau.

Ta rubuta a kasa cewa, “Wannan ne asalin yadda aka fitar da sunayen, kuskuren rubutu ne aka yi sunanki ya shiga.”

Ta kara da cewa, “’Yan jarida ne suka sanya hotunan mutane. Kuskure ba laifi ba ne, kuma hakan ya faru ne saboda wadanda suka rubuta ba ’yan Arewa ba ne.

“Muna da ’yan wasa da suke siyasa da wadanda ba sa siyasa. Mun san ba ki siyasa, amma duk da haka, warware miki shubha ba laifi ba ne.

“Zama cikin masu tallata dan takara ma na da wasu sharudda da sai kin cika kafin a sa sunanki.”

Sai dai Rahama Sadau ta sake mayar da martani, inda ta ce, “Zuwa ga Mansurah Isah, zan so in ba ki shawara ki bar maganar nan kawai ta wuce domin manyanki sun kira sun nemi gafara, inda suka ce kuskure ne.

“Ba sai ki zama mai magana da yawun wani ba.”

Ita kuma jaruma Madam Korede jan hankalin Rahama Sadau ta yi, inda ta ce, “Wallahi Rahama Sadau an taba yi wa Mansurah Isah taron dangi saboda ta ki goyon bayan a ci miki mutunci.”

Sauran wadanda suke cikin jerin sunayen su ne: Fati Nijar da Hadiza Kabara da Samirah Ahmed da Kyauta Dillaliya da Mommee Gombe da Teema Makamashi da sauransu.

AMINIYA