Rasha ta sace daraktan masana’antar nukiliyar Ukraine

0
117

Sojojin Rasha sun yi awon gaba da wani Darakta-Janar da ke aiki a masana’antar nukiliyarta ta Zaporizhzhia.

Gwamnatin Ukraine na zargin dakarun Rasha da azabtarwa da kuma wulakanta babban jami’in a masana’antar nukiliyar da ke yankin Kudancin Ukraine da ke karkashin ikon sojojin Rasha.

“Sojojin Rasha sun yi garkuwa da Mataimakin Darakta-Janar na Sashen Kula da Ma’aikata a Masana’antar Nukiliya ta Zaporizhzhia, Valeriy Martyniuk,” in ji sanarwar da gwamnatin Ukraine ta fitar a ranar Talata.

Sanarwar ta yi kira ga Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) Rafael Grossi da zai kai ziyara Rasha da ya sa baki Rasha ta sako jami’in.