Hukumar Gudanarwar Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), ta karyata rahotannin da ke cewa ta ayyana ranar da za a koma aiki domin ci gaba da gudanar da harkokin ilimi.
Jami’ar Bayero dai ta dakatar da aiki a sakamakon yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’o’in Kasar ta ASUU ta tsunduma watanni takwas da suka gabata.
Cikin wata sanarwa da jami’ar ta fitar a wannan mako, ta ce labaran da ake jingina mata na ayyana ranar komawa bakin aiki ba gaskiya ba ne.
“Muna kira ga dalibai, iyaye da sauran al’umma da su yi watsi da wannan rahoto da yake yaduwa.
“Wannan jita-jita da ake yadawa ba ta da madogara ballantana tushe,” a cewar sanarwar da mai magana da yawun jami’ar, Lamara Garba ya fitar.
Ya jaddada cewa, jama’a musamman dalibai da iyayensu su wofantar da wannan jita-jita da aka kaga da wata manufa ta zalunci.
A kwanakin bayan nan ne dai Shugaban ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana fatansa na kawo karshen yajin aikin nan ba da jima ba.
Farfesa Emmanuel ya bayyana hakan bayan shiga tsakani da Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila ya yi dangane da tankiyar da ke tsakanin ASUU da Gwamnatin Tarayya.
AMINYA