Igbo na da karfin mulkar Najeriya – Gwamna Ortom

0
94

Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya bayyana amincewa da ‘yan kabilar Igbo, yana mai cewa suna da karfin mulkin Najeriya idan aka basu dama.

Gwamnan, wanda ya bayyana hakan a Makurdi, babban birnin jihar a ranar Laraba lokacin da kungiyar ‘yan kabilar Igbo ta PDP Forum ta kai masa ziyarar ban girma, ya ce ‘yan Kudu-maso-Gabas suna karbar baki kuma suna aiki tukuru.

A cewar Ortom, ‘yan kabilar Igbo suna zaman lafiya, yana mai jaddada cewa suna da damar zama da sauran kabilun kasar.

Ya sha alwashin ci gaba da magana da hukuma kan hare-haren da ake zargin makiyaya ne da ke kaiwa mutanen Benue.

“Ibo suna maraba da aiki tukuru. Kungiya ce da za ta iya zama da sauran kabilu ba kamar wadanda ke kashe jama’ata ba, su na so in yi shiru.

“Ba zan taɓa yin shiru ba game da hare-haren da makiyaya ke kaiwa jama’ata ba dare ba rana, har sai hukumomi sun yi abin da ya dace. Zan ci gaba da magana kan rashin adalci,” inji shi.