Rikici ya barke tsakanin kungiyar ASUU kan batun dakatar da yajin aiki

0
72

A dai dai lokacin da ake sa ran Kungiyar Ma’aikatan Jami’o’in na iya janye yajin aikin da ta shiga ranar Alhamis (yau), in da kotun daukaka kara a ranar Juma’ar da ta gabata, ta umurci kungiyar ta janye yajin aikin.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa galibin rassan kungiyar sama da 123 sun kammala taron su na yajin aikin.

Binciken da jaridar PUNCH da ta yi ya nuna cewa yayin da wasu jami’o’in suka kada kuri’ar dakatar da yajin aikin, wasu kuma sun kada kuri’ar cigaba da yajin aikin.

Sai dai jami’ar Obafemi Awolowo, reshen Ile-Ife,  bata cimma matsaya ba.

Wata majiya daga reshen ta ce, “Ba a cimma matsaya ba. Membobin sun amince da bin shawarar kwamitin zartarwa na kungiyar na kasa. Ku tuna, mun yi yajin aiki kafin hukumar ta kasa ta ayyana yajin aikin.”

Al’amarin ya sha bamban a jami’ar Nnamdi Azikiwe, inda daya daga cikin wakilanmu ya tattaro cewa reshen ya kada kuri’ar amincewa da “dakatar da shi bisa ka’ida”.

Sai dai a taron da aka gudanar a Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Akure, wanda kuma ya samu mambobin ASUU daga Jami’ar Adekunle Ajasin, Akungba-Akoko da ke Jihar Ondo, mambobin kungiyar sun kada kuri’ar dakatar da su ne domin kada su bi umarnin kotu.

“Mambobin mu ba su so kada kuri’a tun farko ba amma kun san ASUU kungiyar masu hankali ce kuma ba za a kama mu muna karya doka ba. Shi ya sa muka kada kuri’ar dakatarwa,” wani mamban kungiyar da ya halarci taron ya bayyana wa jaridar The PUNCH.

An kuma tattaro cewa Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta kada kuri’ar dakatar da yajin aikin bisa sharadin.

A Jami’ar Usmanu DanFodiyo, wakilanmu ma sun tattaro cewa, reshen ya kada kuri’ar dakatar da shi ne bisa umurnin kotun daukaka kara.

Sai dai har yanzu ASUU na jiran matakin da shugaban kasa Muhammadu Buhari  zai yanke kan karin albashin malaman jami’o’i.