Rasha za ta gina babbar cibiyar tara gas a Turkiya

0
86

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiya ya goyi bayan shirin takwaransa na Rasha Vladimir Putin game da gina babbar cibiyar tara iskar gas a cikin kasar bayan da shugaban ya bayyana cewa wannan dabara ce da ke bukatar a aiwatar da ita a cikin gaggawa.

Jaridu a Ankara sun ruwaito cewa tun farko shugaba Vladimir Putin ne ya gabatarwa Erdogan shirin, a wani yunkuri na isar da makamashi kudancin Turai ta cikin Turkiya sakamakon matsalar da ake samu a aikin tura iskar gas din ta bututun gas din NordStream.

Tuni dai wannan mataki ya ja hankalin kasashen Turai musamman Faransa inda ofishin shugaba Emmanuel Macron ya fitar da sanarwar da ke sukar matakin wanda ya bayyana yunkurin na Rasha da Turkiya a matsayin abin da ya sabawa hankali.

Rasha wadda dama ita ke bai wa Turkiya makamashin gas ta hanyar bututun TurkStream da ke karkashin bakin teku wanda ya hada kasashen biyu, sabon yunkurin zai saukaka mata fitar da gas zuwa kasashen Turai wadanda ta ke jituwa da su tare zagaye wadanda ta ke takun saka da su.

Erdogan da ke sanar da wannan sabon yunkuri bayan dawowarsa daga ganawa da Putin a Kazakhstan jiya alhamis, ya ce ko shakka babu za a samar da rumbunan adana gas din a mahadar kasashen Turkiya da Bulgaria da kuma Girka.