An hana sama da ‘yan kallo 1,000 kallon kofin duniya

0
102

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta dakatar da sama da mutum 1,300 da aka yanke musu hukuncin dakatarwa daga shiga kallon wasan kwallon kafa daga Ingila da Wales , ba za su je gasar kofin duniya a bana ba.

Tuni aka bukaci da su mika fasfo dinsu hakan na nufin dakile shirin zuwa kallon wasan kofin duniya da Katar za ta karbi bakunci a bana, don kada su tayar da hatsaniya a yayin da ake gudanar da wasannin.

Cikin sababbin matakan da aka dauka da zai fara aiki daga 14 ga watan Oktoban 2022, zai hana duk wani mai goyon bayan da aka samu da laifin tayar da hatsaniya zuwa gasar kofin duniya da za’a buga cikin watan Nuwamba.

Sanarwar ta ce ba za mu bar masu halayya mara kyau, wadanda ke karya doka, domin dakile shirin nakasa babbar gasar kofin duniya ta kwalon kafa da ake sa ran za ta kayatar ” in ji ofishin hukumar ayyukan cikin gida a Burtaniya.

Za’a fara gasar kofin duniya daga 20 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan Disambar 2022 ‘yan sanda za su tilasta wa mutum 1,3008, wadanda aka hana shiga kallon kwallon, bayan samunsu da laifin tayar da yamutsi da su mika fasfunansu.

Duk wanda bai bi doka ba aka same shi da kokarin zuwa kallon gasar kofin duniya – za a yanke masa hukuncin zaman wata shida a gidan gyaran hali da cin tara kuma duk wanda abin ya shafa idan har zai yi bulaguro a lokacin gasar kofin duniya sai ya nemi izini, sannan zai sha binciken inda zai je da abin da zai je yi sannan za’a kuma a tsaurara bincike a tasoshin jirgin ruwa, domin zakulo wadanda ke son karya dokar.