Atiku ya fara kamfen ta fadar sarkin Zazzau

0
120

Dan takarar shugaban kasa karkashin Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya kaddamar da yakin neman zaben sa a Jihar Kaduna.

Atiku Abubakar ya fara ne da kai ziyarar ban girma ga Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli a fadarsa da ke Zariya.

Dan takarar shugaban kasar tare da ayarinsa na yakin neman zaben sun isa fadar ta Zazzau ne da misalin karfe 11.20 na safiyar Asabar.

Da yake jawabi, Atiku ya ce ya je fadar ce domin neman albarka da shawarwari daga mai martaba don samun nasara.

Ya ce shi zuwansa Zariya kamar zuwa gida ne, saboda ya dauki Zariya a matsayin garinsa.

Ya kara da cewa, ziyarar na da nasaba da taya Sarkin Zazzau murna bisa samun lambar girmamawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba shi kwanan nan.

Da yake nasa jawabin, Babban Daraktan Yakin Neman Zaben Atiku kuma Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya ce a tsarinsu na kafen, duk inda suka je sai sun kai ziyara wajen iyayen kasa domin neman albarka.

Ya sanar da cewa, a tsarin tafiyarsu babu batanci ko cin mutuncin ko tozarta wani domin wanzuwar zaman lafiya da hadin kan kasa.

Da yake jawabinsa, Sarkin Zazzau, Mallam Ahmed Nuhu Bamalli, ya yi godiya bisa ziyarar da aka kawo sannan ya hori ’yan siyasa da su kiyaye kalamansu wajen kokarin neman jama’a.

Ya roke su da su hori magoya bayansu da su guji yin abubuwan da za su iya tada hankalin alumma.