Wata budurwa ta kashe saurayinta a Nasarawa

0
77

An damke wata mata mai shekara 30 kan zargin yin amfani da wuka ta kashe saurayinta a yankin Maraba da ke Jihar Nasarawa.

Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya ce, matar ta kashe saurayin nata ne bayan fada ya kaure a tsakaninsu.

Ya ce, yanzu, “Tana hannu kuma an kwace wukar da ta yi amfani da ita wajen aikata kisan, bisa umarnin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Nasarawa, Adesina Soyemi.

A cewarsa, sun damke matar ne bayan ta yi danyen aiki a Ungwan Gwari, Karamar Hukumar Karu ta jihar.

“An mika ta ga Babban Sashen Binciken Manyan Laifuka da ke Lafia domin zurfafa bincike sannan a gurfanar da ita a gaban kotu domin zama izina ga wasu,”  in ji shi.