Faransa za ta horas da sojojin Ukraine 2000

0
99

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya amince da shawarar horar da dimbin sojojin Ukraine a kasar, matakin da ministan tsaro Sebastien Lecornu ya tabbatar, yayin wata hira da ya yi da jaridar Le Parisien a ranar Asabar.

Ministan tsaron Faransar ya ce sojojin Ukraine akalla dubu 2 suke sa ran za su horas, a cigaba da kokarin tallafa musu kan yakin da suke gwabzawa da Rasha.

A ranar Larabar da ta gabata, shugaba Macron yayi alkawarin taimakawa Ukraine da na’urorin garkuwa daga hare-haren makamai masu linzami, da na jirage yaki.

Kasashen yammacin Turai dai na cigaba da taimakawa Ukraine da makudan kudade da kuma makamai, domin dakile mamayar da Rasha ke yi mata, tallafin da ake ganin ko shakkah babu shi ne yake taka rawa wajen nasarorin sake kwato wasu yankuna da dakarun kasar ta Ukraine ke yi daga hannun Rasha a baya bayan nan.